Yunkurin sakin Fursunonin siyasar Kasar Cuba

Taswirar kasar Cuba
Image caption Ministan hulda da kasashen ketare na Spain ya isa Cuba domin dafawa yunkurin sakin fursonin da laifukansu suka danganci siyasa

Ministan hulda da kasashen ketare na Spain, Miguel Angel Moratinos, ya isa Cuba inda zai dafawa cocin Roman Katolika a yunkurin ganin an saki fursonin da laifukansu suka danganci siyasa.

Ciki har da wani mai yajin cin abinci da ke cikin tsananin rashin lafiya GIYERMO FARINYAS da ya ki amincewa a sakeshi har sai an saki sauran tsararrun da ke fama da rashin lafiya.

mutane dari da sittin da bakwai ne ke zaman kurkuku a Cuba bisa laifuffukan da suka danganci siyasa sabanin dari biyu da dayan da ke tsare a bara.

An sami fursunonin da suka mutu sakamakon yajin kin cin abinci ad suka yi abinda ya kara jan hankalin kasashen duniya

Hukumar kare hakkin dan adam ta Cuban wacce bata hukuma ba, ta zargi gwamnatin kasar da take hakkokin bil adama da kuma amfani da wasu hanyoyi wajen hana 'yan adawa fadin albarkacin bakinsu