Gwamnonin bankunan kasashen D8 na taro a Abuja

Nigeria
Image caption Nigeria

Gwamnonin manyan bankunan kasashe masu tasowa takwas, wato D8 suna wani taro a Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya da nufin zakulo hanyoyin da kasashen zasu bi wajen bullowa manyan kalubalen tattalin arziki da kasashen ke fuskanta.

Wannan dai wani share fage ne ga taron shugabannin kasashen takwas wadanda suke da musulmi masu yawa a cikinsu. Kusan dai radadin matsin tattalin arzikin da duniya ta shiga a bara ya fi yin tasiri ne a irin wadannan kasashe, inda aka samu karayar darajar kudadensu da ma raguwar zuba jari daga kasashen waje.