Direba ya kashe leburori shida a Masar

Taswirar Masar
Image caption A baya dai Masar ta sha fama da hare-hare iri daban daban

Rahotannin da ke fitowa daga birnin Alkahira na Masar na cewa wani direban motar Bus ya harbe wasu ma'aikata shida har lahira, kamar yadda kafafen yada labarai na gwamnati suka bayyana.

Kafofin yada labaran suka ce direban wanda ke tuka wasu leburorin zuwa wurin aiki a wajen birnin Alkahira, amma sai kawai ya tsaya inda ya juyo ya budewa fasinjojin nasa wuta.

Kuma nan take ya kashe mutane shida daga cikin su, sannan ya jikkata wasu da dama.

A yanzu dai jami'an 'yansanda sun yi awan gaba da shi kuma kawo yanzu babu wani bayani kan dalilin da yasa direban daukar wannan mataki.

Amma alamu daga wurin da abin ya faru da kuma wadanda aka ritsa da su, na nuna cewa harin ba shi da alaka da siyasa.

A baya dai kasar ta yi fama da hare-hare daga kungiyoyin masu fafutuka, amma al'amura sun dan daidai ta a 'yan shekarun nan.