Jamus ta baiwa manoman Nijer taimakon iri

Niger
Image caption Niger

A jihar Tahoua dake jamhuriyar Nijar gwamnatin kasar Jamus ce ta bada taimakon irin shuka ga manoma.

Wannan taimako da kasar ta Jamus ta kawo ta bada shi ne ga jihohi uku na kasar ta Nijar da suka hada da Maradi, da Tillibery da Tahoua.

Wakilin kungiyar Lucop ta kasar jamus ya Shaidawa BBC cewa yunkurin nasu ya biyo bayan kiran da gwamnatin kasar ta yi ne ne ga sauran kasashen duniya na su tallafawa Nijar din, musamman ma a daidai wannan lokaci na shigar damuna.

Yanzu haka dai manoma na fuskantar matsaloli masu yawan gaske wajen samun ingantaccen irin shuka, da ma abinci da zai ba su damar noma gonakin nasu.