Matsaloli wajen sake tsugunnar da 'yan fafutukar Niger Delta

A Najeriya ana korafin cewa, rashin kyakkyawan tanaji na neman kawo cikas ga ci gaba da shirin gwamnatin kasar, na sake tsugunnar da 'yan gwagwarmayar yankin Niger Delta, wadanda suka amince da shirin afuwa na gwamnatin tarayya.

A karkashin tsarin dai an shirya koyar da sana'o'i ga 'yan gwagwarmaya kimanin dubu 20. An dai fara samun tangarda ne tun daga batun biyan kudaden alawus alawus ga tsoffin 'yan gwagwarmayar.

Tsohon shugaban Najeriyar ne, marigayi Alhaji Umaru Musa 'Yaradua, ya yi ahuwa ga masu fafutuka na yankin Niger Delta, wadanda suka amince su ajiye makamansu.