Isra'ila na son zaman lafiya in ji Obama

Obama da Netanyahu
Image caption Obama da Netanyahu

Shugaba Barack Obama ya ce yayi amannar Isra'ila da gaske take game da batun samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hakan ya biyo bayan wata ganawa ce tsakanin shugaba Obaman da Praministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

A wannan karon, Mr Obama ya yabawa Mr Netanyahu, kan yadda ya sassauta takunkumin da Isra'ilar ta daura wa yankin Zirin Gaza, ba kamar a lokacin ganawar da suka yi ba a cikin watan Mayu, inda ya rika yi masa fuskar shanu.

Shugaban Amirkan ya ce shi da bakon nasa sun tattauna akan matakai na zahiri da ya kamata a dauka a makonni masu zuwa, wadanda za su taimaka wajen komawa shawarwari kai tsaye tare da Falasdinawa, amma bai yi karin bayyani ba.