Gwamnatocin Turai sunyi maraba da sassaucin Israila a Gaza

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Image caption Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Gwamnatocin kasashen Turai na maraba da sassaucin da Israila ta yiwa takunkumin da ta sanyawa zirin Gaza.

A Amurka kuwa inda firaministan Israila Binyamin Netanyahu zai gana da shugaba Obama a yau, kakakin fadar White House ya ce Mr. Obama na fatan tattaunawa kan matakan da za'a dauka na gaba don kawo zaman lafiya a yankin.

Sai dai al'ummar zirin Gazan sun ce sassaucin ya yi kadan ya biya musu bukatunsu.