Sojojin Birtaniya za su fice daga Sangin

Sojojin kasar Birtaniya
Image caption Birtaniya zata janye dakarunta daga yankin Sangin na Afghanistan

Ana sa ran a ranar Laraba sakataren tsaron Birtaniya Liam Fox zai sanarwa da majalisar wakilan kasar cewa dakarun sojan kasar za su mika yankin Sangin,inda anan ne aka fi fafatawa a yakin da ake yi a kasar Afghanistan ga sojojin Amurka.

Babu tantama cewa sakataren tsaron zai fuskancin babban kalubale wajen rarrashin 'yan majalisar Birtaniya da kuma iyalan sojojin kasar 99 da suka rasa rayukansu a yankin na Sangin cewa wannan ba wai ja da baya ba ne na yaki.

Za dai a mika wannan yanki ne a cikin shekarar da muke ciki.

Kimanin dakarun Birtaniya casa'in ne dai suka rasa rayukansu a yankin na Sangin wanda shi ne daya bisa uku na daukacin asarar da kasar ta yi na sojanta tun da aka fara yaki a kasar ta Afghanistan.

Kuma wannan ba shi ne karon farko da dakarun Birtaniya ke mika jagorancin wani yanki da suka fi fuskantar tirjiya ga Amurka ba.

Ko a farkon wannan shekara sai da Birtaniyar ta mika yankunan Kijaki da kuma Musa Qala don kulawarta ga Amurkan.