An damke wani mutum da gawwakin yara

Taswirar Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta tsare wani mutum mai suna Shu'aibu Atanda, bisa zarginsa da kokarin binne gawawwakin kananan yara sittin da shida ba bisa ka'ida ba.

Mutum dai rundunar 'yan sandar da kuma asibitin koyarwa dake jihar Legas suka tabbatar da cewa yana yiwa asibitin kwantiragi ne.

Sai dai a cewar 'yan sandan wanda ake zargin maimakon yaje ya binne gwawwakin yaran a makabarta, sai ya nemi binne su a daji, don yin hakan yafi araha.

Wasu daga cikin gawwakin dai na yaran da iyayensu suka kwashe watanni ba su je sun karbi gawawwakin ba ne.