Libya ta mika karin fursunoni ga Nijar

Taswirar jamhuriyyar Nijar

A jamhuriyar Nijar, a yau wani jirgin sama dauke da fursunoni kimanin dari da ashirin daga kasar Libiya, ya sauka a filin jirgin saman Diori Hamani na Yamai.

A ranar litinin ne wani jirgin ya kawo wasu fursunonin 'yan Nijar kashin farko daga Libiya.

Fursunonin na daga cikin 'yan Nijar din fiye da dari biyar da ake tsare da su a gidajen kason Libiyar bisa zarge zarge iri daban daban.

A yanzu haka dai ana ci gaba da jiran wasu karin fursunonin daga libiyar, bayan wata yarjejeniya da gwamnatocin kasashen biyu suka cimma a watan jiya.