Zaman jin bahasi kan yaki da ta'addanci a Nijeriya

Wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka kashe a Nijeriya
Image caption Wasu 'yan kungiyar Boko Haram da aka kashe a Nijeriya

Majalisar dokokin Nigeria ta fara wani zaman jin bahasi, akan wani kudurin doka na yaki da ta'addanci, da halatta kudaden haram a kasar.

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi da karkatar da kudade ,shine ya kira taron, domin tattaro shawarwarin da za su taimaka wajen karfafawa, tare kuma da zartar da dokokin a kasar.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Nijeria ta'anati, EFCC ta yi marhabin da kudirin dokar, tana mai cewar idan aka zartas da dokar , za ta taimaka ma ta wajen gudanar da ayyukanta.