Tsaffin 'yan gwagwarmayar Niger Delta sunyi bore

'yan gwagwarmaya kafin su ajiye makamai

A Najeria, wasu daruruwan matasa da ke ikirarin cewa su tsofaffin 'yan gwagwarmayan yankin Niger Delta ne, sun yi wata zanga zanga a Abuja.

Matasan cikin jerin gwanon motoci sun nemi shiga cikin birnin domin nuna rashin amincewarsu da yadda ake aiwatar da shirin afuwar da aka yi masu.

Sai dai rahotanni sun ce rundunar 'yan sanda ta Abuja ta katsewa matasan hanzari, gabanin su kai ga shiga birnin.

Jerin gwanon masu gwagwarmayar na yankin Niger Delta ya kawo cikas ga harkokin sufuri akan hanyar da ta taso daga gwagwalada zuwa cikin Abuja.