Musayar fursunoni tsakanin Rasha da Amurka

Wadanda ake zargi da leken asiri
Image caption Wasu daga cikin wadanda ake zargi da yiwa Rasha leken asiri a Amurka

Rahotanni daga Rasha sun nuna cewar hukumomi a kasar na shirin yin musayar fursunoni domin mayar da mutanen nan 10 da aka kama a Amurka cikin a kan zargin yiwa Rashar leken asiri.

Mahaifan wani masanin ilimin kimiyya da aka daure a Rashar a shekara ta 2004 saboda mika wasu asiran soji ga Burtaniya, Igor Sutyagin sunce ya yi masu waya daga wani gidan yari ranar Talata inda yace musu za a mayar da shi Moscow domin shiryawa musayar.

Ya sheda musu cewar yana jin tayin ya fito ne daga Amurka, kuma musayar za ta iya shafar wasu fursunonin a Rasha.

Yayi ikirarin cewa nan da 'yan kwanaki masu zuwa za a fitar da shi daga Rasha zuwa wata kasa, watakila Burtaniya.

Ernst Chernyl, mai fafutukar kare hakkin jama'a ne a kasar Rasha, ya kuma shaida wa wani gidan Radiyo cewar yana sane da batun kokarin yin musayar fursunonin da Mr Sutyagin.

Ya ce: "A karshe an yi masa tayin a tura shi Ingila. Bisa dukkan alamu a gobe za ayi hakan. Sai dai kuma sun sa shi ya rattaba hannu a kan wata takarda, wadda a ciki ya amsa laifin aikata leken asiri".

Don haka na fahimci cewar ba shi da wani zabi. Kuma a kwanakin baya ne aka ki amincewa a sako shi, ya karasa zaman sarkarsa a gida.

'hanzarta warware batun'

Ya zuwa yanzu dai hukumomin Rasha sun ki su tabbatar da cewar ko akwai shirin yin wannan musaya ta fursunoni.

A shekara ta 2004 ne aka yanke wa Igor Santiagin hukuncin daurin shekaru 15, a kan zargin ya mika wasu bayanan sirri na soja, ga wasu kampanonin Burtaniya. Kodayake dai ya sha nanata cewar bayanan da ya mika ba na sirri ne da aka haramta mikawa ba.

Kuma a ranar Talata, jaridar New York Times, ita ma ta rubuta wani labari inda take cewar hukumomin Amurka ma na duba yuwuwar yadda za a hanzarta warware batun nan da ya shafi wasu jami'an leken asirin Rashar. Jaridar ta ce daga cikin hanyoyin, akwai yuwuwar wadanda ake zargi, wadanda ba tare da wata wata ba, suka amsa cewar sun yi wa hukumar leken asirin kasar Rasha ayyukan leken asiri, za a fitar da su daga Amurkar.