Za a gudanar da zabe a jihar Anambra

Taswirar Najeriya
Image caption An shafe shekaru goma sha biyu ba a gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar Anambra ba

Gwamnatin jihar Anambra dake kudu maso Gabashin Najeriya ta ce zata gudanar da zabukan kananan hukumomi a jihar a watan Disamba bayan kwashe shekaru goma sha biyu ba tare da an gudanar da zabukan ba.

An dai kasa gudanar da zaben ne a duk shekarun da suka gabata, saboda rikice-rikicen siyasa da shari'o'in da suka yi ta biyo bayansu a jihar abin da ya tilasta barin al'amuran shugabancin kananan hukumomin a hannun jami'an da gwamnati kan nada.

Sai dai yanzu gwamnati ta ce an samu kwanciyar hankali a jihar don haka ne za a gudanar da zabukan.

Jihar Anambra dai ta yi kaurin suna wajen rikice-rikicen siyasa tun bayan da kasar ta koma ga tafarkin mulkin Dimokradiyya a shekarar dubu da dari tara da casa'in da tara.