Afurka ta kudu ta nemi gafara

Spain ta samu galaba akan Jamus
Image caption Spain ta samu galaba akan Jamus

Gwamnatin Afrika ta kudu ta nemi gafara daga daruruwan masoya wasan kwallon kafa wadanda basu samu damar kallon wasannin da aka buga ranar laraba ba tsakanin Jamus da Spain a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da akeyi a kasar.

Gwamnatin ta ce hakan ya faru ne saboda cunkoson da aka samu a filin saukar jiragen sama na kasar.

Masu kula da al'amura a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Sarki Shaka dake Durban sunce jirage masu zaman kansu dake dauke da manyan baki ne suka rufe inda sauran jirage ke sauka.

Wasu rahotannin na nuna cewa akwai masoya wasan kwallon kafa da suka fashe da kuka, lokacin da suka ga ba za su samu kallon karawa tsakanin Jamus da Spain ba.