Shugabannin kungiyar D-8 sun kammala taron koli

Shugaban Nigeria
Image caption Dr Goodluck Jonathan

Shugabannin kasashe takwas masu tasowa na kungiyar D-8 sun kammala taron kolin da suka yi a Abuja.

Kasashen takwas dake da dimbin yawan musulmi a kasashensu sun yi alkwarin kara hada kai wajen tunkarar manyan matsalolin da suke fuskanta ta fuskar tattalin arziki da makamashi da kuma hada-hadar kasuwanci.

Shugaban Najeriya wadda ta karbi shugabancin kungiyar, watau Dr Goodluck Jonathan yace zai dauki matakan da suka hada da ziyartar wasu kasashen da ke cikin kungiyar domin karfafa manufofinsu.

A wata lakca da ya yi bayan ganawarsu, Shugaban kasar Iran, Mahmud Ahmedinejad, wanda ya halarci taron kolin, ya bayyana cewar babu wani sauyi da kasarsa za tayi a shirinta na nukiiya, duk kuwa da takunkumin da Majalissar dinkin duniya ta sanyawa kasar.