Ma'aikata sun yi zanga-zanga a Ghana

Masu zanga zanga
Image caption Masu zanga zangar neman karin albashi

Wasu kananan ma'aikatan gwamnatin Ghana sun yi wata zanga- zanga yau a birnin Accra, inda suka doshi fadar shugaban kasa domin gabatar da takardar neman karin albashi.

Ma'aikatan suna kokawa ne akan wani sabon tsarin albashi wanda suka ce bai musu dadi ba. Ma'aiktan na neman hukumar dake kula da tsara albashi ta kasa, ta tattauna tare da su kai tsaye.

Ma'aiktan karkashin kungiyar CLOGSAG, sun sha alwashin shiga yajin aiki, idan har gwamnati ba ta amsa kiran da suke yi ba.