An kaddamar da shirin maido da martabar Nigeria a Maiduguri

Farfesa Dora Akunyili
Image caption Ministar yada labarai ta Nigeria

Ministan yada labarai ta Najeriya, Mrs Dora Akunyili, ta jagoranci kaddamar da shirin nan na dawo da martabar Najeriya na shiyyar arewa maso gabashin kasar a Maiduguri jihar Borno.

Kimanin shekara guda kenan da bullo da wannan shiri domin fadakar da jama'a akan yadda zasu yi kokarin gudanar da abubuwan da zasu hana irin mummunan kallon da wasu kasashen ke yiwa Najeriya.

Abubuwan da Najeriyar ta yi kaurin suna akansu sun hada da cin hanci da rashawa da zamba cikin aminci da aikata miyagun laifuka da makamantansu.

Miliyoyin Nairori ne dai Gwamnatin tarayyar ta kashe domin ganin cewar shirin ya samu karbuwa tare da kawo sauyi kan cimma burin da ake bukata.