Tabarbarewar harkar kwallon kafa a Najeriya

Tawagar Super Eagles
Image caption Tawagar Super Eagles ba ta lashe wasa ko guda ba a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na bana

An fidda kasashen duniya da dama daga gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Afrika ta kudu, saboda mummunar rawar da suka taka, amma babu kasar da ta dauki tsatsauran mataki kan habbaka kafa 4kamar Najeriya.

An kori manyan jami'ai uku a Hukumar kwallon kafa ta kasar, wato NFF.

Shugaba Goodluck Jonathan ya yi kokarin dakatar da 'yan wasan kasar daga halartar gasar kasa da kasa na tsawon shekaru biyu, kafin hukumar kula da kwallon kafa ta duniya ta shiga tsakani kuma ta gargadi Najeriyar.

Koma bayan da aka samu a harkar kwallon kafa a Najeriya, ya shafi kusan kowani mataki ne na kwallon kafa a kasar.

"Dakatar da 'yan wasan kasar da kuma dage dakatarwar da shugaban kasar ya yi ba shi da muhimmaci". Inji Churchill Olise, mai kungiyar cibiyar koyar da wasan kwallon kafa na Ebede da ke Shagamu.

"Abu mafi amfani shine shugabanni su san yadda abubuwa su ka kazanta a harkar kwallon kafa a kasar".

Najeriya dai tana da dimbin matasan da suka kware a harkar kwallon kafa, kuma idan aka samu aka yi amfani da su yadda ya kamata, Najeriya za ta yi fice a harkar tamola.

Amma masana a kasar sun yi nuni da cewar, rashin amfani da kwararu da kuma rashin samun kayayakin zamani da zai inganta wasan da kuma ci hanci da reshawa tsakanin jami'ian hukumar NFF na cikin abubuwan da su ka dakushe ci gaban harkar kwallon a kasar.

"Sallamar jami'an NFF somin tabi ne kawai, akwai abubuwa da dama da ya kamata a yi", inji Wilson Ajua, wani lauya kuma mai kungiyar kwallon kafa ta Rainbow FC a Lagos.

"Kamata ya yi shugaban kasa ya kara gyara a harkar kwallon kafar kasar domin ci da harkar kwallon kafa gaba".

Cin hanci da rashawa na cikin abubuwan dake dakushe ci gaba kwallon kafa a Najeriya, abin da kuma ya kai har ga kungiyoyin cikin gida.

"yawancin 'yan wasan kwallon kafa na kungiyoyin cikin gida ba su da kwarewar da ya kamata".

"Ina ganin harkar kwallon kafa a Najeriya ta tabarbare, saboda ana saka siyasa a hakar tafiyar da kungiyoyin cikin gida, a maimakon gudanar da su a matsayin kasuwanci.

Gyara a harkar kwallon kafa

Bayan muguwar rawar da tawagar Super Eagles ta taka a gasar da aka shirya a kasar Afrika ta kudu, Shugaba Goodluck Jonathan ya sanar da dakatar da 'yan wasan kwallon kafa na kasar daga shiga gasa har tsawon shekaru biyu, matakin da ya fusata hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA wacce ta baiwa Nijeriya wa'adin janye wannan dakatarwar ko ta gamu da fushin ta.

Karshe dai Nijeriyar tai amai ta lashe aka janye wannan barzana.

"Shugaba Goodluck Jonathan ya dage dakatarwar da ya yiwa 'yan wasan kasar, saboda yadda mosaya kwallon kafa suka nuna sha'warsu na wasan kuma suka nemi shugaban kasar ya sauya hakan". Inji wata sanarwa da Hukumar NFF ta fitar.

Amma wasu masana a harkar kwallon kafa suna ganin sauya matakin da shugaban kasar ya yi na dakatar da 'yan wasan ba zai tasiri ba ganin irin yadda harkar kwallon kafa ya tabarbare a kasar.