An cafke mutane uku kan ta'addanci a Norway

Shugaban 'yan sandan Norway Janne Kristianesen
Image caption Shugaban 'yan sandan Norway Janne Kristianesen tana bayyana kamen da aka yi

Hukumomi a kasar Norway sun ce an kama mutane ukku da ake zargi da alaka da shirin bom na kungiyar Alqa'ida a duka Amurka da Biritaniya.

'Yansanda sun ce mutanen suna shirya wasu ayyuka ne na ta'addanci.

Kamun ya biyo bayan neman tasa keya ne da aka samu jiya daga Amurka, a kan wani mutum, Abid Naseer, da ake zargi da shirin kai hari a kan wani wuri mai tarin shaguna a birnin Manchester a bara.

An chafke mazan ne dai bayan shafe watanni ana saka idanu akan su. Shugabar hukumar 'yan sandan kasar Norway Janne Kristianesen, ta bayyana cewa sun dade suna nazartar abinda mazan ke yi:

"Tace binciken kamar yadda aka bayyana, an dade ana yinsa, sai dai ba zan ce ko tun yaushe ba."

"A wannan lokacin, an yi ta samun abubuwa da dama, amma sai muka yanke shawarar bin diddigen wadannan mazan na tsawon lokaci," in ji Kristianesen.

Sai dai kuma bayanan da aka samu game da harin da suke shirin kaiwa din basu da yawa.

Shugabar hukumar 'yan sandan wato Janne Kristianesen ta bayyana cewa suna tunanin suna da alaka da kungiyar Al Qaeda:

"Tace a yau ne dai hukumar 'yan sanda ta Norway ta chafke maza uku bisa ga zargin alaka da 'yan ta'adda da kuma niyyar kai harin ta'addanci, tare da yunkurin kai harin ta'addanci".

A jiya ne kuma ma'aikatar shari'a ta Amurka a karo na farko ta alakanta wani yunkuri na tada bam a hanyar jirgin karkashin kasa da kuma wani da aka gano a watan Aprilun bara a birnin Manchester.

Ta dai bayyana cewa duka wannan makarkashiya iri daya ce irin wadda kungiyar Al-Qaeda dake Pakistan ke shiryawa.

Yanzu kuma alamu na nuni da cewa an samo wani bangare na uku na makarkashiyar.