Yaki da cin hanci da rashawa a Jumhuriyar Nijer

Tsohon shugaban kasa Mamadou Tandja
Image caption Ana binciken almundahanar da ake zargi an tafka ne a lokacin mulkin Mamadou Tandja

A jamhuriyar Nijar hukumar da gwamnatin mulkin sojan kasar ta kafa domin kwato kudade da dukiyar kasa da ake zargin wasu shugabannin kasar sun yi sama-da-fadi da su, ta ce ya zuwa yanzu, ta yi nasarar karbo miliyan 600 na kudin CFA, kuma tana ci gaba da bincikenta.

A wata hira da manema labarai yau a Yamai, shugaban hukumar, malam Abdul-Karim Mosi ya ce babu gudu ba ja da baya,hukumar ta su za ta yi aikinta domin kwato wa kasa hakkinta kamar yadda shugaban kasar Janar Salu Jibo ya bayar da umurni.

Hukumar na gudanar da bincike ne a cikin ma'aikatu da kamfanoni da kuma masana'antu na gwamnati kuma tana da cikakken ikon yin haka kamar yadda hukumomin mulkin sojan suka umurta