Majalisa za ta sake yin nazari kan kasafin kudin bana

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya sake mikawa majalisar dokoki ta kasa kudirin yin garambawul ga kasafin kudin kasar na bana.

Wannan kudiri dai na neman rage adadin kudaden da za'a kashe wajen gudanar da ayyukan ci gaban al'umma, da kuma kudin da za'a kashe a bukukuwan cikar Najeriyar shekaru hamsin da samun yancin kai daga Naira biliyan goma zuwa kusan Naira biliyan bakwai.

Hakan dai ya biyo bayan abinda shugaban kasar ya ce, a baya an yi zulake a kiyasin adadin kudin da kasar za ta samu .

Sai dai yayinda wakilan majalisun dokokin ke cewa yawan sauyin na kawo cikas ga ayyukansu, masana tattalin arziki kuwa na ganin babu wanda ake kwara da wannan jan kafar da gwamnati ke yi na tabbatar da kasafin kudin, illa talakawan Najeriya da ke zaman jiran tsammani.