An hallaka mutane hamsin a Pakistan

Wani yaro da harin bam ya ritsa da shi a Mohmand
Image caption An dai sha fafatawa mai zafi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan Taliban a Mohmand

Jami'ai a Pakistan sun ce akalla mutane hamsin ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai a yankin Mohmand.

Fashewar abin ya auku ne a gaban ofishin gwamnati dake wani kauye a yankin.

Wadanda aka yi abin a kan idansu sun ce harin ya rusa kimanin shaguna ashirin, kuma baraguzansu sun binne mutane.

Wani rahoto ya nuna cewa mafi yawan wadanda suka riga mu gidan gaskiyan, mutanen yankin ne da suka taru don ganin wasu jami'an dake aiki a ofishin.

Mohmand yanki ne da aka sha fafatawa mai zafi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan Taliban wadanda suka kama kasa a yankin.