Kasar Amurka ta saki 'yan leken asirin Rasha goma

Jirgin da ke dauke da 'yan leken asirin kasar Rashan da aka kama a Amurka
Image caption Kasashen Amurka da Rasha sun amince da musayar 'yan leken asiri

Kasar Amurka ta saki goma daga ciki 'yan leken asirin kasar Rashan da ta kama a wani mataki da ake gani na musayar 'yan leken asiri ne tsakanin kasashen biyu.

Mutanen sun amince da laifukan da ake tuhumarsu da su bayan da aka gurfanar dasu a wata kotu dake birnin Newyork.

An dai kama mutanen ne a ranar ashirin da bakwai na watan Yunin da ya gabata bayan wani dogon bincike da jami'an leken asirin Amurka suka yi musu.

A nata bangaren,gwamnatin kasar Rasha ta gafartawa hudu daga cikin 'yan leken asirin Amurkar da ta kama a baya.