'Yan jarida zasu yi yajin aiki a Italiya

Firaministan Italiya,Silvio Berlusconi
Image caption 'Yan jarida za su fara jayin aiki a Italiya

'Yan Jaridu a kasar Italiya zasu shiga wani yajin aiki don nuna adawa a kan shirye shiryen gwamnatin kasar na kara tsaurara dokokin satar sauraron bayanai ta hanyar amfani da waya.

Ana sa ran yajin aikin zai kawo dakatar da duk wasu shirye shirye a kafafan yada labarai na Rediyo, da Talbijin,har ma da Jaridun kasar.

'Yan Jaridun sun yi zargin matakin zai kawo musu cikas wajen gudanar da bincike, sai dai Prime Ministan kasar Silvio Berlusconi, ya ce 'yan jaridun na shisshigi da yawa a rayuwar jama'a.

'Yan jarida dai suna fuskantar kalubale da dama a duniya dangane da yadda suke gudanar da ayyukansu