ANPP ta zargi PDP da kaiwa sakatariyar ta hari a Zamfara

Shugaban Jam'iyyar PDP na Nijeriya
Image caption Shugaban Jam'iyyar PDP na Nijeriya

Rahotanni daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na cewa zaman tankiyar siyasa ya kara zafi tsakanin ya'yan jam'iyyar PDP mai mulkin jihar da kuma na babbar jam'iyyar Adawa ta ANPP bayan da wasu da ba'a san ko su wane ne ba, suka kona hedikwatar jam'iyyar adawar da tsakar daren jiya.

Rahotanni sun ce haka ma an raunata mutane hudu a harin, wadanda yanzu haka ke karbar magani a wani a asibiti.

Jam'iyyar ANPP dai ta zargi jam'iyyar PDP da anfani da wadanda ta kira yan ta'adda wajen kaiwa sakatariyar ta ta hari.

Sai dai jam'iyyar ta PDP ta musanta cewa tana da hannu a lamarin.