Mutumin da ake farauta a Birtaniya ya mutu

Motar 'yansanda na rakiya ga motar da ta dauki Raoul Moat bayan arangamarsa da 'yansanda
Image caption 'Yansanda sun shafe sa'o'i shida suna kokarin shawo kan Raoul Moat ya mika wuya

Farautar dan bindiginan nan da ake nema ruwa a jallo a kasar Birtaniya ta kawo karshe bayan ya kashe kansa.

Raoul Moat ya kashe kansa ne bayan 'yan sanda sun kwashe sa'o'i kusan shida suna kokarin shawo kansa ya mika wuya.

Jami'an 'yansanda sun tabbatar da cewa Mista Moat ya mutu ne a asibiti da misalin karfe biyu da minti ashirin na daren Juma'a sakamakon harbin kansa da yayi a inda 'yansanda dauke da makamai suka yi masa kawanya.

Mista Moat ya ranta a na kare ne bayan ya harbe tsohuwar budurwarsa da sabon saurayinta har lahira, sannan kuma ya raunana wani dansanda, mako guda da ya gabata.

Wani bawan Allah ne dai ya kyankyasawa 'yansandan cewa ya ga wani mai kama da mutumin da suke farautar a kauyen Rothbury da ke Northumberland a arewacin Ingila.

Wannan ne dai karo na biyu a 'yan makwannin da suka gabata da aka samu faruwar irin wannan al'amari a Birtaniya, inda ba kasafai masu aikata laifi kan yi amfani da bindiga ba.