Rikici ya kunno kai a jam'iyyar CPC ta Kano

Janar muhammadu Buhari, kusa a jam'iyyar CPC
Image caption Shugabannin CPC sun ce masu korafi ba mabiya Janar Buhari ne na gaskiya ba

A Nigeria, wani rikici na neman kunno kai a cikin sabuwar jam'iyyar CPC reshen jihar Kano.

Sabanin dai ya fara ne tun bayan da aka sauke shugabannin jam'iyyar na riko na farko, aka kuma maye gurbinsu da wadansu.

Wadansu 'ya'yan jam'iyyar dai sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da shugabancinta suna zargin shugabannin na riko da kokarin tsayar da wadanda ransu yake so a takara yayin zabukan badi, ba tare da barin dimokuradiyya ta yi halinta ba.

Tubabben mataimakin shugaban jam’iyyar a Kano ta Kudu, Abdulmalik Danbilki Kwamanda, ya ce wannan rikici ya samo asali ne daga abin da ya kira son zuciyar wadansu daga cikin shugabannin jam’iyyar.

“Duk wani mutum da ba ya ra’ayinsu, to ba zai zama shugaba ba.

“Idan kuma ka nuna kana ra’ayin wani, to ina tabbatar maka a yau sai sun cire ka daga shugabanci.

“Suna da ‘yan takararsu wadanda suke ganin [tsayar da su] zai zama masu alheri; ko mutane suna so ko ba sa so dole za su yi karfa-karfa, saboda Janar Muhammadu Buhari zai zo ya daga hannun dan takara”, inji Abdulmalik Danbilki Kwamanda.

Sai dai shugabannin jam'iyyar sun musanta wannan zargi, suna cewa wadanda ke da'awar rikicin ba ma 'yan jam'iyyar ba ne.

A cewar Alhaji Ahmadu Haruna Zago, shugaban jam’iyyar na riko a Jihar Kano, “a jam’iyyar CPC babu rigima...duk wanda ka ga yana rigima a cikinta yanzu ba dan CPC ba ne.

"Duk wanda ka ga yanzu ya kawo rudu a cikinta, ina tabbatar maka cewa da ma ba ya bin Muhammadu Buhari tun farkonsa zuwa yanzu”.

Jam’iyyar ta CPC dai, za a iya cewa sabanin sauran takwarorinta wadanda ba a jin korafe-korafe a cikinsu har sai sun kafa gwamnati, ta fara ne da rikice-rikice—wadanda suka yi awon gaba da shugabanninta na riko na farko—tun kafin a je ko ina.