An fara babban taron Jam'iyyar Moden Lumana a Nijer

Niger
Image caption Niger

A jamhuriyar Niger dazu an bude babban taro ko CONGRES na jamiyyar Moden-LUMANA-FA-AFFRICA , a karon farko, tun bayan kirkiro wannan jam'iyya a bara.

Wannan babban taro dai nada manufar zaben shugaban jamiyyar na dindindin tare da tsayar da dan takarar shugaban kasa a zabukan da majalisar mulkin sojan CSRD za ta shirya a watan Janairu mai zuwa.

Ana dai hasashen cewa jam'iyyar za ta tsayar da tsohon Firaministan kasar, Malam Hama Amadou a matsayin dan takarar ta na zaben shugaban kasar.

A watan jiya ne dai, Malam Hama Amadu ya yanki tikitin shiga jam'iiyar ta Modem Lumana, bayan da da ya sha kaye a shari'ar da ya yi da bangaren Malam Seini Umarou game da shugabancin jam'iyyar MNSD-Nasara.