Mutane 100 sun mutu a Pakistan

Ana zakulo wadanda suka yi rauni a kunar bakin waken daga baraguzan gine-gine
Image caption Fiye da mutane dari ne suka rasa rayukansu a yankin Mohmand na kasar Pakistan

Mutane fiye da dari ne suka halaka ya zuwa yanzu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a yankin Mohmand na kasar Pakistan a ranar Juma’a.

An gano karin gawarwaki a cikin baraguzan gine-gine, sannan kuma wadansu sun cika a asibiti sakamakon raunukan da suka yi.

Yanzu dai an tabbatar da cewa mutane biyu ne suka kai harin— daya daga cikinsu dai na kan babur ne yayin da ya tayar da bam din dake jikinsa.

Bam na biyu kuma ya tarwatsa shaguna ne sannan ya lalata wani gidan yari.

A yankin Mohmand ne dai aka yi kazamin batakashi tsakanin dakarun Pakistan da ’yan Taliban.