'Yan bindiga sun bude wuta a Afghanistan

Afghanistan
Image caption Afghanistan

Wasu 'yan bindiga da ba a tantance ko su wane ne ba, sun bude wuta a kan wata motar safa a Gabashin Afghanistan, kusa da iyaka da Pakistan, tare da hallaka wasu 'yan Shi'a na Pakistan su sha daya.

Wani kakakin gwamnan lardin Paktia ya ce motar safar ta yi zagaye ne ta shiga cikin Afghanistan, don kaucewa wani yankin mai hadarin gaske a Pakistan.

A yawancin lokuta dai, hare-haren da masu fafutuka na Pakistan ke kaiwa, suna jefa matafiya cikin hadari a wasu yankuna na kaasar ta Pakistan, abun da ya sa motocin ke zagaye, har su shiga cikin Afghanistan.

Wakiliyar BBC ta ce har yanzu dai ba a san ko wane ne ke da alhakin kai harin ba, amma ana kyautata zaton aikin masu fafutuka 'yan Sunni ne, wadanda keda da alaka da 'yan Taliban na Afghanistan.