An fara sakin fursunonin siyasar Cuba

Fidel Castro na gaisawa da wata ma'aikaciya
Image caption Daya daga cikin hotunan Fidel Castro da aka wallafa a intanet, yana gaisawa da wata ma'aikaciyar cibiyar binciken kimiyya

’Yan uwan bijirarrun ‘yan siyasar da ke gidajen kaso a kasar Cuba sun ce an sako kashi na farko na fursunonin a karkashin wata yarjejeniya da aka kulla da gwamnatin kasar.

Wadansu daga cikin ’yan uwan mutanen sun ce an shaida masu cewa an tafi da ’yan uwan nasu zuwa Havana, babban birnin kasar.

Majami’ar Katolika ta ce akalla fursunoni goma sha bakwai ne suka amince su bar kasar zuwa kasar Spaniya.

Babu bayani a hukumance a kan ko mutane nawa ne aka saki a wannan kashin na farko, to amma a ranar Laraba hukumomin kasar ta Cuba sun yi alkawarin sakin bijirarru hamsin da biyu kwata-kwata.

A halin da ake ciki kuma, wadansu ’yan jaridar kasar ta Cuba su biyu sun wallafa sababbin hotunan tsohon shugaban kasar, Fidel Castro, a intanet.

Hotunan sun nuna Mista Castro yana murmushi, kuma ga alamu yana cikin koshin lafiya, inda yake magana da ma’aikata a wata cibiyar binciken kimiyya da ke Havana.

Rabon da a dauki hoton Mista Castro a bainar jama’a tun kafin ya kwanta rashin lafiya a shekarar 2006, ko da yake wasu hotunan sun nuna shi yana ganawa da wadansu manyan jami’an kasashen waje masu ziyara a kasar a asirce.