Takaddamar majalisa da gwamnatin Kenya

Shugaba Mwai Kibaki na Kenya
Image caption 'Yan Majalisar dokokin Kenya sun yi barazanar kin amincewa da kasafin kudin kasar har sai gwamnati ta kara masu albashi

'Yan majalisar dokokin Kenya sun yi barazanar kin amincewa da kasafin kudin kasar har sai ministan kudi ya amince ya kara masu albashi.

A makon da ya gabata ne dai 'yan majalisar suka amince da wani rahoto wanda ya bukaci a yi masu karin kudi, al'amarin da zai sa su shiga sahun 'yan majalisar da ke daukar albashi mafi tsoka a duniya.

Ya zuwa yanzu dai ministan kudin, Uhuru Kenyata, ya ki amincewa da wannan bukata; hakan kuma ya jawo tayar da jijiyoyin wuyar da ka iya kawo tsaiko a gudanar da harkokin gwamnati.

Wannan dai wani fito-na-fito ne a siyasance.

A bangare daya dai akwai 'yan majalisar dokokin na Kenya wadanda a makon jiya suka yi ittifaki a kan sai an masu karin kashi daya bisa uku na albashinsu.

Hakan kuma zai sa su rika daukar albashin da ya haura na 'yan majalisun dokokin Amurka, a kasar da yawancin ma'aikatanta ke daukar kusan kashi uku cikin dari na albashin ma'aikata a Amurka.

A daya bangaren kuma akwai gwamnati, wadda ta ki amincewa ta shigar da wannan bukata cikin kasafin kudin kasar.

A gefe kuma suna kallo mutanen kasar ne, wadanda wannan bukata ta fusatasu, kuma ranar Alhamis din da ta gabata suka yi gangami zuwa majalisar dokokin don nuna fushinsu.

Mutanen da suka taru a kofar majalisar sun yi ta ihu suna cewa “ba za mu yi musu kari ba; zaluntarmu su ke yi; barci ma suke yi a majalisar”.

'Yan majalisar dai sun ce ba su da zabi illa su yiwa kansu karin albashin.

A watan gobe ne dai mutanen kasar za su kada kuri'a a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda idan suka amince da shi, to a karo na farko 'yan majalisa za su fara biyan haraji.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dai sun ce tuni suka shiga halin kuncin rayuwa, balle kuma an dora musu harajin kashi talatin cikin dari na albashinsu.

Bangarorin biyu dai na ci gaba da hararar juna, ko da yake an fara tattaunawa a kan hanyoyin warware matsalar.

To amma tuni kimar 'yan siyasa ta zube a idon al'ummar kasar ta Kenya.