An sabunta: 12 ga Yuli, 2010 - An wallafa a 15:45 GMT

Al-Shabab ta dauki alhakin harin Uganda

Wadanda suka samu rauni a harin bom din Uganda

Fiye da mutane saba'in ne suka hallaka yayin da da dama suka samu raunuka

Kungiyar 'yan kishin Islama ta Al-Shabab ta dauki alhakin harin bom din da aka kai a Kampala, babban birnin kasar Uganda.

A kalla sama da mutane sama da saba'in ne suka hallaka, lokacin bama-bamai biyu suka tashi a lokaci guda, sa'ilin da mutane ke kallon wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya.

A wata sanarwa da suka fitar a birnin Mogadishu, mai magana da yawun kungiyar ta Al-Shabab yace kungiyar na yakar duk wanda ke adawa da ita, ko a ina yake.

A baya dai kungiyar Al-Shabab ta yi kiran da a kai hari kan Uganda, saboda gudunmawar da ta bayar ta dakaru ga rundunar kiyaye zaman lafiya ta Tarayyar Afrika da aka tura Somaliya, wadda suka zarga da kai hare hare kan fararen hula.

Jami'an tsaro a Uganda sun zargi mamabobin kungiyar da laifin kai harin, wanda ya faru a loakcin da jama'a ke kallon wasan karshe tsakanin Spaniya da Holand ranar Lahadi.

'Yansandan Uganda sun ce sun gano gawarwakin mutane biyu da suke kyautata tsammanin 'yan Somaliya ne, kuma ana zaton su suka kai harin, amma kawo yanzu babu wasu shaidu da suka tabbatar da hakan.

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.