Kungiyar yaki da bauta ta bude asusun taimako a Nijer

A jihar Tahoua dake jamhuriyar Nijar kungiyar nan ta Timidriya, mai fafutukar yaki da bauta, ta bude wani asusun taimako.

A lokacin da aka kirkiro wannan asusu, ta ce ta yi shi ne domin amfanin 'ya'yanta kafin daga bisani ta fadada shi zuwa ga daukacin al'umar yankin, wanda a baya yayi kaurin suna wajen wannan dabi'a ta sa aikin bauta.

Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne da zimmar hana matasa ketarewa zuwa wasu kasashe don neman kudi , ta hanyar ba su bashi, domin yin sana'o'i a cikin kasa .