Lauyoyi hamsin sun kai EFCC kara kotu

Nijeria
Image caption Nijeria

A Nijeriya, a yau ne wasu lauyoyi masu zaman kansu a kasar su hamsin suka shigar da kara gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja inda suke neman kotun da ta tursasawa hukumar EFCC don ganin ta gurfanar da duk wasu da ke da hannu a zargin cin hanci a kwangilar nan ta Halliburton.

Ita dai wannan badakala ta cin hanci, ta kai ga an daure wasu mutane tare da cin tarar kamfanin a Amurka, bayan da suka amsa baiwa wasu masu fada aji a Nijeriya toshiyar baki domin samun kwangila.

Su dai wadannan lauyoyin sun zargi hukumar EFCC ne da jan kafa wajen gurfanar da wadanda ake zargin suna da hannu a al'amarin, zargin da hukumar EFCC ta musanta.