Bama-bamai sun kashe mutane sittin a Uganda

Wasu daga cikin mutanen da suka yi rauni a Uganda
Image caption Bama-baman sun tashi ne a wuraren da aka taru ana kallon wasan kwallon kafa

Fiye da mutane sittin ne ake fargabar sun rasa rayukansu sakamakon tashin wasu bama-bamai guda biyu a Kampala, babban birnin kasar Uganda.

Jami'an 'yansandan Ugandan sun dora alhakin fashewar da bama-baman a kan masu tayar da kayar baya na Somaliya.

An tashi daya daga cikin bama-baman ne a wani mashahurin gidan cin abinci na Habashawa da ke unguwar Kabalagala a wajen garin Kampala, dayan kuma a wani kulob din wasan rugby da ke tsakiyar birnin.

Tashin bama-baman kuma ya zo ne a daidai lokacin da ake wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya; kuma a wuraren da kan cika da 'yan kallo.

Shugaban 'yan sandan Uganda, Kale Kaihura, ya ce akwai yiwuwar 'yan tawayen al-Shabab na Somaliya ne suka kai hare-haren.

A baya dai kungiyar ta al-Shabab, wadda ake zargin tana da alaka da Al Qa'ida, ta yi barazanar za ta kai hari a Kampala saboda goyon bayan da Uganda ke baiwa gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya.

Sojojin Uganda ne dai suka fi yawa a cikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afirka, wadda ta ke ba gwamnatin Somaliya kariya.

Kasancewar daya daga cikin wuraren da aka kai harin mallakar 'yan kasar Habasha ne ya kara karfafa wannan tunanin ganin cewa ita ma Habashan ta taka muhimmiyar rawa wajen hana kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci karbe mulki a Somaliya.

To amma har yanzu babu wata hujjar da ke tabbatar da wanda ke da alhakin kai hare-haren; yayinda wasu ke cewa tayar da bama-baman na da alaka da zabukan da za a yi badi a Ugandan.