Cutar Kyanda ta bulla a kasar Zambia

Shugabankasar Zambia Rupiah Banda
Image caption An sami rahotannin bullar cutar kyanda a kasar zambia inda mutane dubu uku suka kamu

Jami'an kiwon lafiya a kasar Zambia sun bada rahotannin bullar cutar kyanda a kasar. Jami'an sun kuma ce mutane kusan da dubu uku ne suka kamu da cutar cikin watanni shiddan farkon wannan shekarar .

Dan haka jami'in kiwon lafiyan kasar, Peter Mwaba yace daga wannan makon ne za'a soma allurar riga kafin cutar a babban birnin kasar wato Lusaka, inda nan ne aka fi samun wadanda suka kamu da cutar ta kyanda.

Masu aiko da rahotanni daga kasar Zambian sun dora alkahin rashin nasarar daake samu dangane da kamfen din yaki da cutar sakamakon rashin isassun kudade