Spaniya ta lashe gasar cin kofin duniya

Spaniya ta lashe gasar cin kofin duniya
Image caption Wannan shi ne karo na farko a tarihi da Spaniya ta lashe wannan gasa

Kasar Spain ta lashe gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Afrika ta Kudu bayan da ta doke Holland da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Soccer City.

Spain din dai ta sami nasara ne a karin lokaci bayan an kammalla mintina casa'in na farko.

Jama'a a kasar sun yi ta buki cikin dare har wayewar gari domin nuna farin cikinsu kan nasarar da kasar ta samu a gasar ta bana.

Yanzu kasar Spaniya ta kafa tarihi inda ta zama kasa ta takwas a cikin jerin kasashen da suka taba cin gasar.

Kasashen dai su ne, Uruguay da Jamus da Brazil da Ingila da Argentina da Italiya da Faransa, yayin da Spain din ta zama kasa ta takwas.

Masu lura da al'amuran yau da kullum na ganin Spain din ta cancanci yin nasara a gasar musamman ganin irin kwallon da ake takawa a kasar, sannan ita ce ta ke rike da kambun nahiyar Turai.

Kasar Holand din ita ma ta yi kokari sosai a wasan, inda ta sami dama amma ba ta iya amfani da ita ba.

Wannan shi ne karo na uku da Holland ta kai zagayen karshe amma ba ta iya daukar kofin ba.

Maraba

Dubban jama'a ne suka taru a filin saukar jiragen sama na birnin Madrid domin yin maraba da tawagar 'yan kwallon Spaniya bayan da suka isa gida daga Afrika ta Kudu inda suka lashe gasar cin kofin duniya.

Kyaftin din kasar Ike Casilas ne ya fara saukowa daga cikin jirgin inda yake rike da kofin, sannan sauran 'yan wasan suka biyo shi.

Image caption Jama'a sun yi ta murna cikin dare a kasar ta Spaniya

Firaministan kasar Zapatero, ya bayyana nasarar da suka samu da cewa wani abu ne da ba za a manta da shi a tarihin kasar ba.

Yayin da kociyan kasar Vicente Del Bosque, ya ce nasarar da kasar ta samu wata nasara ce ga kasaitacciyar ledar da suke takawa.

Wannan shi ne karo na farko da kasar ta lashe wannan gasar, kuma ta kafa tarihi ganin cewa ita ce ke rike da kanbun zakarun turai, wanda ta lashe a shekara ta 2008.

Daga bisani 'yan wasan sun garzaya zuwa cikin gari, inda dubban daruruwan jama'a suke jiransu domin yi musu maraba.

Murna

An ci gaba da murna tun farkon dare har wayewar gari, inda jama'a suka yi ta shaye-shaye da kade-kade a Madrid babban birnin kasar.

Jama'ar wadanda suka rufe jikinsu da tutocin kasar sun rufe manyan titunan birnin na Madrid, abinda ya janyo tsaiko ga harkokin zirga zirga.

Har ila yau 'yan kasar ta Spaniya da ke zaune a kasashen duniya daban-daban, da suka hada da Argentina da Amurka da Pakistan, sun yi ta murna suna shewa sakamakon wannan nasara.

Hatta a nahiyar Afrika ma inda aka gudanar da gasar a karon farko, 'yan wasan Spaniyan sun samu goyon baya sosai daga wurin jama'ar nahiyar.

Image caption Thomas Mueller na Jamus ne matashin dan wasan da ya fi kowa a gasar

Waiwaye adon tafiya

Wasan karshe na gasar cin kofin duniyar da aka fafata ranar Lahadi tsakanin kasashe biyu na Turai wato Holand da Spaniya, alama ce ta yadda nahiyar ta mamaye gasar ta bana.

Duk da cewa da farko ana tunanin kasashen Kudancin Amurka ne za su lashe gasar, amma daga bisani sai labari ya sha ban ban.

Haduwar kasashen turai a wasan karshe wani abu ne da ba a zaci faruwarsa ba a farkon gasar.

Faransa da Italiya wadanda suka buga wasan karshe a gasar data gabata, sun kasa samun nasara a wasa ko daya, abin da yasa aka fitar da su a zagayen farko.

Itama Ingila bata kayatar da 'yan kallo ba, hatta Spaniya ma an doketa a wasan farko. Yayin da kasashen Afrika suma suka gaza, amma a bangare guda takwarorinsu na Kudancin Amurka sun taka rawar gani.

Image caption Tun a zagayen farko na gasar ne dai aka fitar da mai rike da kanbun Italiya

'Yan wasan Argentina sun ware nan da nan, inda suka rinka zira kwallaye. Alamu sun nuna Brazil ma ta samu kanta, tana da 'yan baya da kuma 'yan gaba sosai. Paraguay da Uruguay da Chile duk sun taka rawar gani a rukunansu.

A kasashen turai Jamus da Holand ne kawai suka nuna alamun za su iya yin wani abu na azo a gani a gasar.

Amma sai al'amura suka sauya a lokaci guda. Kasashe hudu ne suka halarci zagayen dab dana kusa da karshe daga Kudancin Amurka, amma Uruguay ce kawai ta tsallake.

Masana sun yi maganganu da dama kan dalilan da suka sa kasashen Turai suka warware a gasar bayan sun yi lakolako a farko.

Spaniya da Holand basu kayatar da 'yan kallo da wata leda ta azo agani ba. Mai yiwuwa fahimtar juna da kuma sa'a ce ta taimaka musu.

Abin da ya fito fili dai a yanzu shi ne Spaniya ta lashe gasar cin kofin duniya a karon farko a tarihi.

Image caption Diego Forlan ne dan wasan da yafi kowanne taka leda a gasar ta bana

Kyaututtuka

Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta bayyana dan wasan Uruguay Diego Forlan, a matsayin dan wasan da ya fi kowanne taka leda a gasar cin kofin duniya ta bana.

Haka za lika dan wasan Jamus Thomas Mueller, ya lashe kyautar matashin dan wasan da ya fi kowanne taka leda a gasar.

Haka kuma hukumar FIFA ta bayyana Mueller, dan shekaru 20, a matsayin wanda ya fi kowa zira kwallaye-bayan da ya zira kwallo biyar-sannan ya taimaka wajen zira kwallaye uku.

Dan wasan na Jamus ya doke Forlan da David Villa na Spaniya da Wesley Sneijder na Holand domin samun wannan kyauta, wadanda suma suka zira kwallaye biyar-biyar.

Yayinda Forlan ya doke dan wasan Holand Sneijder da maki 23.4% a kuri'ar da 'yan jaridu na duniya suka kada, yayinda dan wasan Spaniya David Villa ya zo na uku.

"Wannan kyautar da aka bani, godiya ce ga sauran 'yan wasanmu," a cewar Forlan, kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Twitter, inda ya ke dauke da hoton kyautar da aka ba shi.

Haka kuma an zabi mai tsaron gida na Spaniya Iker Casillas-wanda sau biyu yana hana Robben zira kwallo, golan da ya fi kowanne nuna bajinta a gasar, inda aka bashi kyautar safar zinare.