An samu kashe-kashe a Taraba da Filato, Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption 'Yan sanda suna ci gaba da bincike

Rundunar 'yan sanda ta jihar Taraba a Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar mutane hudu da kuma jikkata wasu da dama a rikicin addinin da aka yi a garin Wukari.

Rahotanni daga Wukarin sun bayyana cewa kura ta lafa bayan rikicin addini da ya barke, inda aka wayi gari ana jin amon harbe harben bindigogi, da kuma kone-konen dukiya.

An dai ce rikicin ya taso ne bayan rusa wani masallaci da aka yi.

‘Yansanda kuma sun ce bas u yi kame-kame ba tukuna game da wannan rikici, amma akwai yiwuwar a yi hakan a nan gaba

Haka kuma, jami'an tsaro na hadin gwiwa a Jihar Plateau sun tabbatar da mutuwar mutane uku a garin Federe, yayin da kuma kimanin mutane goma sha biyu, ciki har da hakimin garin suka jikkata.

Wannan dai ya biyo bayan kai wa gidan Hakimin garin farmaki ne da wadansu dauke da makamai suka yi a daren jiya.

Barkewar wannan rikici a jihar ta Plateau da ta dade tana fama da tashin hankali, ya sa gwamnatin Jihar ta bayyana rashin jin dadinta game da yadda ta ce jami'an tsaro na hadin gwiwa suka kasa samar da zaman lafiya a jihar.

Sai dai kuma su jami'an tsaron sun bayyana cewa suna iya bakin kokarinsu.

Jami’an tsaron sun ce musabbabin rikicin na gidajen sarautar garin ne, ba na addini ko kabilanci ba.