An tuhumi wasu 'Yan sandan New Orleans da kisan kai

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption An tuhumi wasu 'yan sanda biyu a birnin New Orleans na kasar Amurka da laifin kisa bayan aukuwar mahaukaciyar guguwar nan na Katrina a shekarar 2005

An tuhumi wasu 'yan sanda hudu bisa laifin harbe wani yaro dan shekara sha bakwai a birnin New Orleans, bayan mahaukaciyar guguwar nan ta Katrina ta daidaita birnin a watan Satumbar shekara ta 2005.

Wannan lamari dai ya raunana hudu daga cikin iyalan yaron, kuma wadannan 'yan sanda suna fuskantar wata tuhumar ta daban dangane da harbe wani mai tabin hankali.

Kuma 'yan sanda da dama sun amsa cewar, sun taimaka wajen yin rufafa dangane da wannan lamari.

Idan har aka sami 'yan sandan da laifi, maiyiwuwa za'a yanke masu hukuncin kisa

Mahaukaciyar guguwar dai a wancan lokacin tasa 'yan sanda sun kauracewa yankunan da suke aiki abinda yasa sauran masu samar da tsaro sukai ta kokarin dawo da doka da oda