Kamfanin BP ya soma aikin gwaji

Kamfanin mai na BP ya soma yin wani gwaji mai muhimmancin gaske a kokarinsa na sa marufi da zai toshe rijiyar man dake yoyo a cikin tekun Mexico, domin gano ko marufin yana da karfin da zai iya hana malalar man.

Aikin sa marufin dai ka iya daukar awoyi da dama, kuma tuni gwamnatin Amurka ta amincewa kamfanin na BP ya cigaba da wannan gwaji, bayan tun farko an samu fargabar cewar, aikin ka iya yin illa maimakon gyara.

Tun watan Aprilu ne dai mai ke malala a tekun Mexico, bayan wani bututun mai ya balle, lamarin da ya kai ga hallaka mutane goma.