Injiniyoyin mai na BP sun gyara inda mai ke tsiyaya

Injiniyoyin kamfanin man BP sun gyara wani wurin da mai ke tsiyaya, a rijiyar man da ta lalace a yankin ruwan Mexico.

Wani jami'in da ke kula da yadda aikin ke gudana, ya ce a yanzu suna yin wasu gwaje-gwaje, domin ganin ko gyaran yayi.

Idan har an dace, to hakan zai kawo karshen malalar da mai ke yi a teku.