Masanin kimiyyar Iran sauya sheka ya yi-in ji Amruka

Wani jami'in gwamnatin Amurka ya shaidawa BBC cewa masanin kimiyyar nukiliyar Iran din nan, wanda bai dade da komawa gida ba, ya sauya sheka ne, amma daga bisanai ya sauya ra'ayi, domin yana kewar iyalansa.

Jami'in ya ce , masanin kimiyyar, Shahram Amiri ya baiwa Amurka wasu muhimman bayanai, masu tushe.

Ya ce, an baiwa Mr Amiri makudan kudade, amma ba zai iya taba su ba a yanzu, a sakamakon takunkumin tattalin arzikin da aka daura ma kasarsa.

Shi dai a wani taron manema labarai a Tehran; Mr Amiri ya ce sace shi aka yi; Ya ce, jami'an asiri na Amurka da Saudiyya ne suka sace ni, a gaban otel din da na sauka a birnin Madina.

Sun kai ni wani wuri da ban sani ba a Saudiya.

Sai dai Amurkar ta ce wannan furuci nasa tatsuniya ce.