Bangalesh tace a fitar da littattafan Abul A'ala Maududi daga masallatai

Gwamnatin Bangladesh ta bada umarni ga masallatai da dakunan karatu a duk fadin kasar da su kwashe dukkan wasu littafai da fitaccen malamin nan mai ra'ayin sauyi, Syed Abul A'ala-Maududi ya rubuta.

Ana yi wa Sheikh Maududi, jagoran jam'iyyar masu ra'ayin Musulunci, ta Jama'at-e-Islami, a matsayin na gaba gaba a yankin wajen bada fatawa kan nuna kaifin ra'ayin Islama.

Wani babban jami'i a jam'iyyar da Jammat-e-Islami ya bayyana matakin da cewa yaki ne da Musulunci.

Sai dai jami'an gwamnatin Bangladesh na cewa rubuce rubucen Sheikh Maududi na kara jaddada kaifin kishin Islama.