Ba zan tsaya takara a zaben 2011_ inji Namadi

Image caption Nigeria

Mataimakin shugaban kasar Najeriya ya ce ba zai fito takara ba zaben badi

A Najeriya, Mataimakin shugaban kasar Architect Namadi Sambo, ya nesanta kansa daga wadanda ke kiransa ya fito takarar shugabancin 'kasar a zaben badi.

A cewar mataimakin shugaban kasar, abin da ke gabansa yanzu shi ne inganta rayuwar jama'ar Najeriya, ta hanyar samar musu da ababen more rayuwa.

Malam Umar Sani mai taimakawa mataimakin shugaban 'kasar ne ta fuskar yada labarai, ya shaidawa BBC cewa masu kiran mataimakin shugaban Najeriyar ya tsaya takarar shugabancin 'kasar a zaben 2011, basu yi masa adalci ba.