Supeton Najeriya ya nemi hadin kan sarakunan gargajiya

Supetan yansanda ya nemi hadin kan sarakunan aladun gargajiya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kaddamar da wani gangamin fadakar da sarakunan gargajiya na shiyyar kudu maso gabashin kasar,kan matsalar sace mutane ana garkuwa da su bisa neman fansar kudi, al'amarin da a yanzu ya yi katutu a yankin.

Wannan wani sabon yunkurin ne, wanda mista Obonna Onovo ya kaddamar da kansa domin shawo kan matsalar sace mutane wadda tayi katutu a yankin kudu maso gabashin kasar.

Supetan yansandan ya fada musu cewa duk abubuwan dake faruwa dangane da sace mutane, da sanin wasu daga cikin su akan haka ya wajaba su baiwa yansanda hadin kai, wajen shawo kan wanan matsala.

A ranar Lahadin da ta gabata wasu 'yan bindiga suka sace wasu 'yan jarida hudu da direban motarsu, a kusa da garin Aba na jihar Abiya, bisa neman fansar kudi Naira miliyan dari biyu da hamsin.