Kamfanin BP ya ce zai cigaba da sa ido akan rijiyar mai a tekun mexico

Image caption wasu ma'aikata dake aikin tsaftace tekun Mexico

Jami'in Amurka da ke kula da yunkurin tsayar da kwararar man da ke malala a mashigin tekun Mexico ya ce kamfanin BP zai cigaba da sa ido kan murfin da ya sanyawa rijiyar man zuwa karin kwana guda sakamakon shakkun da ake kan irin matsin da murfin zai iya jurewa.

Wakiliyar BBC ta ce kawo yanzu, babu alamun rijiyar na yoyo don haka mai yiwuwane ta fara kafewa.

Burin kamfanin BP dai shi ne murfin ya hana zubar man, yayin da suke haka kananan rijiyoyin da za su janye mai daga wacce ta samu matsalar.

Hukomomin Amurka sun ce da zarar an kamala gwaje gwajen, jiragen ruwa zasu fara aikin kwashe mai daga rijiyar, sai dai jama'a na cigaba da nuna damuwa akan tsawon lokaci da aikin zai dauka.