BP ya samu karin karfin gwiwa a kan malalar mai

Rijiyar mai a karkashin teku
Image caption Ana fata toshewar ta tabbata

Kampanin mai na BP ya ce yana kara samun kyakkyawan fatan cewa, sabon murfin da aka rufe rijiyar man nan da ta fashe a tekun Mexico da shi, zai ci gaba da hana man fesowa, har zuwa lokacin da za a toshe rijiyar baki daya.

Doug Suttles babban jami'in ayyukan kampanin na BP, ya ce:

“Muna fatan cewa idan abubuwa suka ci gaba kamar yadda suke, muka kuma ci gaba da gudanar da gwaje-gwajen, zamu kai matsayin da zamu kahe rijiyar ga baki daya.”