Jam'iyyar PDP reshen Kano ta fada cikin rikicin

Shugaban jam'iyyar PDP, Osekwelize Nwodo
Image caption Shugaban jam'iyyar PDP, Osekwelize Nwodo

Wasu mambobin jam'iyyar PDP reshen jihar Kano sun nemi a sauke shugabannin jam'iyyar bisa zargin rashin sanin makamar aiki da kuma nuna son kai wajen tafiyar da al'amuran jam'iyar.

'Ya'yan jam'iyyar da ke adawa da shugabannin sun gabatar da korafinsu ne ga shugabannin jam'iyyar ta kasa dake Abuja.

Amma a nasu bangaren, shugabannin jam'iyyar, sun musanta wannan zargi.

Jam'iyyar PDP a Kano ta dade tana fama da rikici iri daban daban, tsakanin magoya bayan tsohon gwamna dakta Rabi'u Musa Kwankwaso dana marigayi Alhaji Abubakar Rimi, abinda yasa wasu ke ganin shi ne ummul aba'isin koma bayan da jam'iyyar ke fuskanta.

Masu lura da al'amura dai na ganin muddum jam'iyyar bata shawo kan matsalolin na ta ba, to zai yi wuya tayi wani katabus a zaben na badi.